in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitattun labarai daga jaridun Najeriya
2016-05-13 20:12:11 cri
Za mu fara da jaridar Guardian wadda ta larabto cewa, a yau Jumma'a gwamnatin tarayyar Najeriya, ta fara aiwatar da kasafin kudin kasar na shekara 2016, inda ta sakarwa ma'aikatu, sassa da hukumomin kasar kudaden gudanar da ayyukansu. Sannan ta umarce su da su rika gabatar mata da rahoton yadda suka tafiyar da ayyukansu a kowa ne wata.

Ita kuma jaridar Punch ta wallafa cewa, yanzu haka ana canja kudin kasar wato Naira a kan dala 341,hakan ya faru ne sakamakon tallafin man da mahukuntan kasar suka cire a ranar laraba, inda aka umarci manyan dillalan mai da su sayar da man a kan farashin da bai wuce naira 145 kan kowa ce lita.

Daga karshe a nata labarin jaridar Daily Trust ta labarto cewa,ministar Kudi ta Najeriya Kemi Adeosun ta umarci da a gudanar da bincike kan albashin da ake biyan sojojin kasa, sama da kuma na ruwan kasar, domin abin ta kira gudun canja akalar albashin jami'an na wata-wata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China