Alamu na nuna cewa, a wannan mako gwamnatin tarayyar Najeriya tana shirin watsi da tsarinta na kayyade farashin mai tare da cire tallafin da ta ke baiwa harkar mai, domin baiwa 'yan kasuwa masu zaman kansu damar shigo da man da kuma sayar da shi a kan farashin da ya dace.
Tun ba yau ba dai bangaren man kasar ke fama da wani sabon kalubale na samar da man, inda ake fama da dogayen layuka a gidajen mai, lamarin da sanya 'yan kasuwa da dama suke sayar da man daga lokaci zuwa lokaci a tsakaninsu, kamar yadda jaridar Guardian ta wallafa.
Ita kuma jaridar Daily Trust ta ruwaito mai rikon mukamin kakakin babban bankin kasar Isaac Okorafor na cewa, babban bankin Najeriyar ya fara gudanar da wani bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar zarge-zargen da ake yi wasu bankuna kasuwancin kasar game da halatta kudin haram.
Daga karshe jaridar Vanguard ta ce 'yan tawayen Niger Delta(NDA) suna shirin kai hare-haren kan batutan mai a Lagos, da Abuja, Fatakwal da kuma Kalaba.(Ibrahim)