Kungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas a Njaeriya (PENGASSAN) ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya, da ta kawo karshen ayyukan 'yan tawaye da fasa batutan mai da ke faruwa a yankin Niger Delta mai arzikin mai.
Shugaban kungiyar Francis Olabode-Johnson wanda ya yi wannan kiran jiya Lahadi a garin Kalaba da ke kudancin kasar, ya ce akwai bukatar gwamnatin kasar Najeriya ta kara zage damtse a yakin da take yi da masu fasa batutan man da satar mai a yankin duba da yadda lamarin ke kara kamari.
Ya ce, gwamnatin kasar Najeriya tana asarar dimbin kudaden shiga sakamako yadda 'yan tawayen ke ci gaba da fasa batutan man. A saboda haka, akwai bukatar mahukuntan kasar da manyan kamfanonin da ke aikin hako mai a yankin, su yi amfani da fasahohi na zamani wajen sa-ido kan batutan man da yadda ake satar danyen man.(Ibrahim)