in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron kolin tsaro na shiyya a Nijeriya
2016-05-15 12:34:59 cri
A jiya Asabar 14 ga wata, shugabannin wasu kasashen Afirka, da suka hada da Nijeriya, da Kamaru, da Nijer, da Chadi, da Benin da sauransu, da kuma shugabannin wasu kasashen yammacin duniya sun gudanar da taron kolin tsaro na shiyya a birnin Abuja, hedkwatar Nijeriya, inda suka yi shawarwari kan yadda za a tinkari ayyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram da sauransu.

Mahalarta taron suna ganin cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasa da kasa sun sami ci gaba a fannin yaki da kungiyar Boko Haram, amma kamata ya yi su ci gaba da kokari, da zummar kawar da wannan kungiya baki daya.

Shugaban Faransa, François Hollande ya bayyana a gun taron kolin cewa, kungiyar Boko Haram na daya daga cikin kungiyoyin duniya da suka fi yin barazana ga bil'adam, wadda ke da alaka da kungiyar IS. Yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a fannin yaki da ita na da muhimmanci kwarai da gaske.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen Birtaniya, Philip Hammond ya furta cewa, ban da daukar matakan soja, kamata ya yi kasashen duniya su kara kokarinsu a fannin yaki da kungiyar Boko Haram. A wannan rana, ma'aikatar harkokin waje ta Birtaniya ta ba da sanarwar cewa, kasar za ta bayar da kudin agaji Pound miliyan 40 ga Nijeriya a cikin shekaru hudu masu zuwa, domin yaki da kungiyar Boko Haram, cikin har da kudin horar da sojojin Nijeriya 1000 domin shiga aikin soja a yankin arewa maso gabashin kasar Nijeriya.

A ranar Jumma'a 13 ga wata, kwamitin sulhun MDD ya ba da sanarwar yin Allah wadai da kai harin ta'addanci da ma sauran danyun ayyukan da kungiyar Boko Haram ta yi a yankin tabkin Chadi, kuma ya kalubalanci sojojin kasa da kasa a wurin domin kara karfin yaki da kungiyar Boko Haram yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China