in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje kolin motoci na kasa da kasa a Najeriya
2016-04-30 12:48:20 cri
A ranar Alhamis data gabata ne aka bude bikin baje kolin motoci na kasa da kasa karo na 11 a birnin Legas a tarayyar Najeriya, inda a lokacin bikin aka nuna nau'o'in sabbin motoci masu yawan gaske.

Sama da motoci sabbin kira kala 100 ne aka nuna, kuma bikin ya samu halartar manyan dillalan motoci daga kasashen duniya da suka hada da Jamus, da Amurka, da Japan, da Indiya, da China, da Faransa, da kuma Najeriyar.

Manajan kamfanin kamfanin hada motoci na Beiqi Foton na kasar Sin da ke Nijeriya, Feng Baoquan, ya shedawa kamfanbin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, kamfaninsa yana hada motoci ne bisa fasahohin zamani na duniya kuma ya samu karbuwa a matakin kasa da kasa.

Za'a cigaba da bikin ne har zuwa ranar 4 ga watan Mayu mai zuwa, kamar yadda masu shirya biki suka tabbatar da hakan.

An fara wannan bikin bajekolin motocin na Lagos International Automobile Exhibition ne tun a shekarar 2005, kuma bikin yana bada dama ga manyan kamfanonin motoci nuna samfurin motocinsu a Najeriya wacce ta kasance kasa mafi yawan alumma a nahiyar Afrika.

Najeriyar ta sha alwashin samar da kashi 80 cikin 100 na kamfanonin hada motoci a cikin gida nan da shekarar 2023, domin rage shigo da kayayyaki daga kasashen waje, da kuma samar da hanyoyin samun kudaden shiga domin rage dogaro kan albarkatun man fetur.

Kasar ta kuduri aniyar hada motoci dubu 500 a duk shekara nan da shekaru 5 masu zuwa, sama da motoci dubu 10 da kamfanonin ke hadawa idan aka kwatanta da shekarar 2014.

Dama dai shugaba Muhammadu Buhari na kasar, ya lashi takobin samar da kashi 50 cikin 100 na kudaden shigar kasar wadanda basu shafi man fetur ba. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China