Mista Adewole ya shaidawa manema labarai haka ne a birnin Abuja, hedkwatar Najeriya,yana mai cewa gwamnati ta bullo da wani shiri mai inganci da za a aiwatar na tsawon shekara guda don ganin an kawar da wadannan cututtuka a Najeriya.
A cewar WHO, wadannan cututtukan suna yaduwa ne ta hanyoyi daban daban da ake samu a yankuna masu zafi kimanin 149 kuma suna shafar mutane fiye da biliyan guda, don haka lamari ne mai cikin kudi sosai ga kasashe masu tasowa na miliyoyin dalar Amurka a wannan shekara.
Cututtukan da ake samu a wurare masu zafi wato MTN da kungiyar WHO ta bayyana sun hada da basir din Buruli, tsutsar ciki, kuturta, ciwon gwiwa, kurkunu, cutar haukan kare, dundumi da dai sauransu kuma suna yaduwa a cikin kasa. (Maman Ada)