Ita kuma jaridar Punch ta wallafa labarin da ke cewa, gwamnan jihar Edo a tarayyar Najeriya Adams Oshiomhole ya zagin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da fifita gwamnonin jihohi na jam'iyyarsa a lokacin da ya ke mulki, inda tsohon shugaban kasar ya baiwa wadancan gwamnoni tallafin kudi har Naira biliyan 2, kimanin sama da dala Amurka miliyan 10 kowanne, daga asusun kare muhalli na kasar ba tare da baiwa takwarorinsu na jam'iyyar APC ba..
Daga karshe sai jaridar Guardian,wadda ke cewa, da alamun hukumar kwallon ta kasar za ta kai ruwa rana da kulob din kwallon na Arsenal, dangane da kin barin dan wasanta mai suna Alex Iwobi ya bugawa Najeriya a gasar Olympics na shekara 2016 da za a yi a birnin Rio.
Rahoranni na nuna cewa, kocin kulob din na Arsenal Wenger ba ya son barin dan wasan mai shekrau 19, saboda muhimmancin sa a kulob din.(Ibrahim)