Uganda ta bukaci Amurka da kada ta sake shakkun sakamakon zabe
Gwamnatin kasar Uganda ta bukaci a ranar Alhamis ga jakadan kasar Amurka da kada ya sake kawo shakku game da nasarar shugaba Yoweri Museveni a zaben watan Febrairun da ya gabata. Kakakin gwamnatin kasar, mista Ofwono Opondo, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa jakadan Amurka madam Deborah Malac na cigaba da jaddada korafe korafenta kan kurakurai a lokacin zaben shugaban kasa. Haka kuma, ya bayyana cewa wasu tsirarrun kungiyoyi a Amurka da Turai, da ma wasu jami'an diplomasiya a kasar Uganda, na cigaba da zuba kudade ga mutanen 'yan adawa bisa manufar janyo wani canjin ta gwamnatin da ba ta sahihanci. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku