A wannan rana, an bude bikin nuna fasahohin kamfanin Huawei a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda, inda ministan ya bayyana cewa, a shekarun baya baya nan, Sin da Uganda sun samu nasara kan hadin gwiwar a fannin sadarwa. Ana gudanar da aikin hada yanar gizo a kasar Uganda wanda gwamnatin kasar Sin ta samar da rancen kudi kuma kamfanin Huawei na Sin dake kasar Uganda ya dauki nauyin gudanarwa don cimma burin kafa yanar gizo a babban birnin kasar da manyan yankunan kasar, aikin da yanzu ya kai ga mataki na uku. Bayan da aka gama aikin, za a sa kaimi ga yin mu'amala a tsakanin hukumomin gwamnatin kasar Uganda, da kananan hukumomin gwamnatin kasar, da kyautata ayyukan gwamnatin kasar ta fannin bautawa jama'a da dai sauransu. (Zainab)