in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun ceto mutane 275 daga hannun Boko Haram
2016-04-06 10:22:14 cri

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar a ranar Talata cewa, ta ceto mutane 275 daga hannun kungiyar Boko Haram a wani samamen da sojojin suka kai a jihar Borno.

A cewar wata sanarwa ta bakin kakakin rundunar, Sani Usman, sojojin sun kashe mayakan kungiyar 15 tare da cafke wasu kusoshin kungiyar 6 a yayin wannan samame na ranar Litinin.

Ya bayyana cewa, sojojin sun samu taimakon jami'an tsaro masu farin kaya da su kai su har mabuyar mayakan.

Haka kuma sojojin Najeriya sun gano wata ma'ajiyar makamai tare da sanya hannu kan albarusai da motocin da 'yan Boko Haram suke amfani da su, a lokacin wannan aiki na soja.

Kungiyar Boko Haram ta kashe dubun dubatar mutane musammun a arewa maso yammacin Najeriya, tun lokacin da ta fara borenta a shekarar 2009, bisa kokarin kafa kasar musulunci.

Sojojin kasar sun kwato yankuna da dama dake karkashin mayakan kungiyar Boko Haram, amma duk da haka kungiyar na ci gaba da kai hare-hare a cikin kasar, tare da fadada ayyukanta a kasashen Kamaru, Chadi da Nijar dake makwabtaka da Najeriya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China