Fatma Samoura, Ko'odinetar sashen jin kai ta ofishin MDD dake Najeriya, ta tabbatar da hakan a jiya Alhamis a birnin Maiduguri na jahar Borno a yayin wata ziyara.
Tace bankin duniyar yayi alkawarin bada dala miliyan 800 ne domin aiki farfado da muhimman ababan more rayuwa da kuma kafa masana'antar sarrafa shara a shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Samoura , tace MDD zata ci gaba da goyon bayan yunkurin bankin duniya da kungiyar tarayyar turai EU, domin shawo kan matsalolin dake haifar da talauci a shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar. (Ahmad)