Mista Clerides ya bayyana cewa bukatar Masar na tasa kiyar Seif Eldin Mustafa, mai shekaru 59, za'a duba ta bayan kammala bincike bisa laifin da aka aikata a cikin tsarin shari'a na hukumonin Cyprus.
Mista Clerides ya ce, "Da zaran bincike ya kammala, to za'a yanke shawara idan har akwai bukatar tasa keyarsa zuwa kasar Masar".
Haka kuma ya kara da cewa za'a dauki wannan mataki bayan shawarwari tare da gwamnati ganin cewa wani mataki ne da siyasa ta shiga ciki.
Mustafa ya bayyana cewa ya karkarta akalar jirgin saman bisa burin ya sake ganin tsohuwar matarsa dake Cyprus, wadda ya rabu da ita a shekarar 1994.
Amma duk da haka, a saukar jirgin saman a Larnaca, ya bukaci Masar da ta saki mata 69 da ake tsare dasu a cikin gidajen kurkukun kasar. (Maman Ada)