A cewar kamfanin dillancin labarai na AMNA, mutumin ya tilasawa matukan jirgin sauka a kasar Cyprus, bayan da ya yi garkuwa da wasu fasinjojin dake cikin jirgin kirar MS181, na kamfanin Alexandria-Cairo a Talatar nan.
Kafin aukuwar wannan lamari dai mutumin ya taba aurar wata 'yar kasar Girka mai zaune a Cyprus, suka kuma haifi 'ya'ya hudu kafin su rabu. An ce mutumin ya bukaci a gabatar da wata takarda ta musamman ga matar ta sa. Har ila yau rahotanni sun nuna cewa tsohuwar matar ta sa, ta isa filin jirgin saman Larnaca, domin taimakawa masu shiga tsakani, kubutar da wadanda ya yi garkuwa da su.
Da fari dai mutumin ya yi barazanar ta da bama baman dake jikin sa, muddin jami'an tsaro suka yi amfani da karfi wajen kubutar da wadanda ya yi garkuwar da su, sai dai daga bisani ya amince da sakin daukacin mutanen.
An ce jirgin fasinjan na dauke ne da mutane 56, da kuma ma'aikan sa 8.
Gabanin hakan hukumomin Masar da na Cyprus sun bayyana daukar matakan da suka dace domin kubutar da daukacin fasinjojin dake jirgin. (Saminu Hassan)