Game da wannan lamari, hukumar gudanarwar kwallon Kwando ta kasar Cuba, ta ce matakin da NBA da takwarar ta ta FIBA suka dauka, na horas da karin matasa a fannin wasan kwallon Kwando abu ne mai matukar amfani.
Rahotanni sun nuna cewa cikin shirin hukumar ta NBA, hadda tsarin gyara filayen wasan kwallon Kwando 3, da bada horo ga matasa a fannin wasan a yankuna 2 dake birnin Havana.
A nasa tsokaci, shugaban hukumar FIBA Horacio Muratore, bayyana godiyar sa yayi game da wannan dama da aka samarwa matasan kasar ta Cuba, matakin da zai tallafa matuka ga masu sha'awar wasan kwallon kwando. Ya kuma tabbatar da cewa za su yi hadin gwiwa da NBA wajen cimma nasarar da aka sanya a gaba.
Wannan dai shiri zai gudana ne karkashin tsarin hukumar NBA, da hadin gwiwar FIBA, tare da goyon bayan hukumar wasanni ta kasar Cuba. (Saminu Alhassan)