in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Arsenal ta doke Norwich City, Newcastle ta haye Relegation
2016-05-04 18:15:35 cri
Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta doke Norwich City da ci 1 da nema a wasan gasar firimiya da suka buga a ranar Asabar. Wannan nasarar da Arsenal ta samu na zuwa ne a gabar da magoyan bayan kungiyar ke shirin gudanar da wata zanga zangar nuna rashin gamsuwa da takun kungiyar. Sakamakon hakan Norwich ya yi kasa a teburin gasar zuwa mataki na 19, bayan da Newcastle da Sunderland suka yi nasarar lashe wasannin su a ranar ta Asabar.

Duk da cewa Arsenal na da ragowar wasanni biyu, tuni ta yiwa West Ham dake biye da ita tazara a matsayi na 6 da maki 8, yayin da ita kuma West Ham ke da ragowar wasanni 3, sai kuma Manchester United dake matsayi na 5 wadda ke da ragowar wasanni 4 a gasar ta Firimiyar kasar Ingila.

Kungiyar Norwich, na biye da Sunderland da maki daya, kana kuma maki biyu bayan Newcastle. Newcastle dai ta samu damar barin siradin relegation a karon farko tun bayan watan Fabarairu, bayan da ta doke Crystal Palace da ci 1 da nema a wasan da suka buga a St James' Park.

A wasan Sunderland da Stoke City sun tashi kunnen doki 1-1, duk da cewa hakan ba zai raba su da jerin kungiyoyi 3 dake kasan teburin gasar ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China