in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jirgin saman kamfanin Masar ya sauka bayan da aka yi fashi da shi
2016-03-29 15:40:50 cri

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Cyprus suka bayar, an ce, an yi fashi da wani jirgin sama na kamfanin jiragen saman kasar Masar a yau Talata, yanzu jirgin saman ya sauka a filin jiragen saman Larnaka dake kudu maso gabashin kasar Cyprus.

Labarin ya kara da cewa, samfurin jirgin saman shi ne Airbus 320, ya kamata ya tashi daga birnin Alexander zuwa Alkahira na kasar Masar, inda akwai fasinjoji da ma'aikata kimanin 60 a cikin jirgin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China