Kamar yadda wata majiya ta tabbatar ma kamfanin dillanci labarai na Xinhua, makasudin wannan aikin shi ne rage kudin da kasar ke kashewa a lantarki. Yanzu haka akwai fitilun kan tituna guda 7,042 da aka rigaya aka kafa a manyan titunan kasar ta Togpo a kashin farko. Ana sa ran kashi na biyun zai fara a watan Satumba mai kamawa wanda za'a kafa fitilu 5,958.
A cewar Abiyou Tcharabalo, daraktan makamashi a ma'aikatar makamashi da ma'adinai, aikin na daga cikin tsarin da kasar ta Togo ta dauka domin inganta sabon shirin yin amfani da makamashi kuma an tsara shi ne ma kasashen duniya da zummar rage kudin lantarki da ake biya a unguwanni.
Aikin samar da lantarkin tituna a kasar Togo shi ne mafi girma kuma wanda aka biya kudi sosai a kan shi, idan aka kwatanta da sauran ayyukan da kamfani ZTE a kasashen Benin, Burkina faso, Niger, Nigeriya, Djibouti da kuma Senegal.
Kamfanin ZTE dai ita ce a kan gaba a bangaren samar da kayayyakin sadarwa a kasar Sin. Yanzu haka tana da shekaru 15 na kwarewar aiki a wannan bangaren. (Fatimah Jibril)