A cewar kakakin gungun 'yan adawar kasar ko SPLM-IO William Ezekiel, a baya an tsara komawar mataimakin shugaban kasar Juba ne a ranar Litinin din nan, bayan ya bar sansanin Pagak. Kana da zarar ya isa birnin Juba a gobe Talata, zai yi rantsuwar kama aiki nan take. (Saminu Alhassan)