A jiya Juma'a ne dai shugaban na Najeriya ya rattaba hannu kan kasafin kudin kasar na bana wanda adadinsa ya kai naira triliyan 6 da biliyan 600 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 30 da miliyan 400, bisa kiyasin gangar danyen mai kan dala 38 a kan kowace ganga.
Sannann an tsara kasafin kudin ne bisa hasashen samar da ganga miliyan 2 da dubu 200 na danyan man a kowace rana a kasar.
Bikin sanyan hannu kan kasafin kudin ya samu halartar mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, da na wakilai Yakubu Dogara da shugaban jam'iyyar APC mai mulki John Odigie-Oyegun.
A yayin jawabinsa, shugaba Buhari ya nuna farin cikinsa game da sanya hannu kan kasafin kudin kasar, sannan ya yabawa bangaren majalisun dokokin kasar bisa hadin kan da suke baiwa bangaren zartaswa.(Ahmad Fagam)