Sirika, ya tabbatar da hakan ne a lokacin taron manema labaru a Abuja, babban birnin kasar, sannan ya gargadi al'umma da su yi hattara don gudun fadawa hannun bata gari wadanda ke amfani da sunansa domin damfarar jama'a ta hanyar shafukan sada zumunta.
Ministan ya ce sama da shafukan facebook da na twitter 20 ne aka bude da sunansa da hotunnasa, har ma ana amfani da shafukan wajen sanar da cewar yana raba Babura da wasu kayayyakin inda ya ce sam bashi da masaniya a kai.
Ya ce yana tabbatarwa duniya cewa ya kauraewa shafukan facebook da twitter da ma sauran shafukan sada zumunta, sannan ya musanta ikirarin da wasu ke bazawa cewa yana raba ayyukan yi ta hanyar internet.(Ahmad Fagam)