in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaitattun labarai daga wasu jaridun Najeriya
2016-05-05 18:53:31 cri
Gwamnatin Najeriya ta ware wasu muhimman sassa 34 da za ta baiwa muhimmanci tun daga kasafin shekarar nan ta 2016. Karamar ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasar Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan, bayan kammala taron majalissar zartaswa, wanda mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Shugaban Muhammadu Buhari na Najeriya, ya ce babu bukatar nuna damuwa, game da yankin Bakassi, domin Najeriya za ta yi cikakkiyar biyayya ga dokokin kasa da kasa, game da hukuncin da aka yanke kan yankin.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne ga shugaban kasar Kamaru Paul Biya, yayin ziyarar da shugaban na Kamaru ya gudanar a Najeriya. Kalaman na shugaba Buhari na zuwa ne a gabar da ake zargin cewa har ya zuwa yanzu Najeriyar na hakar albarkatun danyan mai daga yankin, duk kuwa da cewa kotun kasa da kasa ta mika yankin ga kasar Kamaru.

Shugabannin biyu sun kuma amince da musayar firsunonin Boko Haram tsakanin su, domin gudanar musu da shari'a a kasashen su na asali, kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.

Ministan lafiya na tarayyar Najeriya Isaac Adewole, ya bayyana kyakkyawan fatan sa game da cimma nasarar kawar da cutar zazzabin cizon sauro ko Maleria daga kasar, yana mai cewa gwamnatin kasar mai ci ta dukufa, wajen aiwatar da matakai da za su ba da damar cimma wannan kuduri.

Wasu jami'ai 6 ciki hadda sojojin ruwa 4 sun rasa rayukan su a jihar Bayelsa, biyowa bayan wani harin bazata da aka kai musu. Rahotanni na cewa wasu mahara ne suka kaddamar da harin kan Jami'an a ranar Talata a yankin Nembe dake karamar hukumar Nemben jihar ta Bayelsa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China