Ministan masana'antu,cinikayya da zuba jari na Najeriyar Okey Enelamah ne ya bayyana hakan jiya Alhamis yayin da yake jawabi a gaban majalisar wakilai a ci gaba da muhawarar da ake gami da dabarun sake fadada hanyoyin tattalin arzikin kasar.
Ya ce, dokokin da aka tanada game da tafiyar da harkokin kasuwancin kasar suna da tsauri, don haka wajibi ne su hanzarta yiwa irin wadannan dokokin gyaran fuska ta yadda za a samar da yanayin da ya dace ga masu sha'awar zuba jari a kasar.
A cewar ministan, akwai bukatar a yiwa dokar nan da ta shafi kamfanoni da harkokin sana'o'in hannu, dokar hukumar jiragen kasa da hukumar gidan waya garambawul, ta yadda za su dace da zamani.
Bugu da kari, ministan ya bukaci 'yan majalisun da su hanzarta sanya hannu kan dokar nan ta hukumar daidaita manyan dakunan adana kayayyaki da hada-hadar kadarori, ta yadda kanana da matsakaitan masana'antu za su rika samu kudaden tafiyar da ayyukansu cikin sauki. Kuma hakan zai ba da damar zuba jari a bangaren kayayyakin more rayuwar jama'a.
Ministan ya kuma bayyana cewa, Najeriya za ta fadada tunaninta game da bangaren kayayyakin more rayuwa kasancewarsu jigon da za su kara samar da yanayin zuba jari a kasar. (Ibrahim Yaya)