in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta biya dukkan kudi ga MDD cikin lokaci
2015-12-25 19:53:49 cri
A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa duk rana a yau Jumm'a 25 ga wata, Mr. Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi bayani game da yawan kudin da ya kamata kowace mambar MDD ta biya da na aikin shimfida zaman lafiya. Mr. Lu ya bayyana cewa, a matsayin wata kasa mai son sauke nauyin da aka dora mata, kuma mambar din din din ta kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin za ta ci gaba da sauke nauyin da aka dora mata kan batun kasafin kudi da ya kamata kowace mambar MDD ta biya, kuma za ta biya dukkan kudin da ya kamata ta biya ga MDD.

A ranar Alhamis 23 ga wata ne, a yayin babban taron MDD, aka zartas da sabon rabon yawan kudin da ya kamata kowace mambar MDD ta biya wa MDD da na aikin shimfida zaman lafiya a duniya. Bisa sabon rabon da aka kebe wa kasar Sin, cikin shekaru biyu masu zuwa, yawan kudin da ya kamata ta biya wa MDD za ta kai kashi 7.921 cikin kashi dari bisa na jimillar kudin da ya kamata a biya wa MDD, sannan yawan kudin shimfida zaman lafiya da ya kamata kasar Sin ta biya zai kai kasha 10.2 cikin dari bisa na dukkan kudin shimfida zaman lafiya da MDD za ta samu. Sakamakon haka, kasar Sin ta zama daya daga cikin kasashe uku bayan Amurka da Japan wadanda suke biya kudin aiki mafi yawa ga MDD, kuma tana matsayi na biyu bayan Amurka wajen samar da kudin shimfida zaman lafiya a duk duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China