in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Najeriya ta canza dabarun yaki don murkushe Boko Haram kafin karshen Disamba
2015-10-08 09:24:30 cri
Rundunar sojin Najeriya ta sauya dabarun yakin da take yi da mayakan Boko haram domin murkushe kungiyar kafin nan da watan Disamba kamar yadda shugaba Muhammadu Buhari na kasar ya ba su umarni.

Babban hafsan tsaron kasar Gabriel Olonisakin ne ya bayyana hakan ga manema labaru a larabar nan a birnin Fatakol mai arzikin man fetur.

Ya ce suna cigaba da bullo da sabbin dabaru iri dabam dabam domin murkushe kungiyar kafin cikar wa'adin da shugaban kasar ya diba musu.

Idan dai za'a iya tunawa, a watan Ogasta ne, shugaba Muhammadu Buhari ya umarci dakarun Najeriyar da su kawar da kungiyar Boko Haram cikin wadatanni 3.

Kungiyar Boko Haram, ta hallaka mutane sama da dubu 13 tun lokacin da ta fara kaddamar da hare haren ta a Najeriya a shekarar 2009.( Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China