Ministan yada labarai da raya al'adu na kasar Lai Muhammad ne ya bayyana aniyar gwamnatin a sakonsa na bikin ranar 'yan jarida ta duniya, wanda aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata a Abuja fadar mulkin kasar.
Minsitan ya ce dokar ta FOI za ta kasance a matsayin wani muhimmin makami da za'a yi amfani da shi wajen yaki da rashawa da kuma samar da budaddiyar gwamnati a kasar.
Lai Muhammad ya ce, gwamnati ta dauki wasu kwararan matakai bama ga tabbatar da 'yancin fadin albarkacin baki ba, har ma da ba da damar samun muhimman bayanai. (Ahmad Fagam)