in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci a tanadi dokar kisa kan masu mafataucin jama'a
2016-05-05 09:31:04 cri
A jiya Laraba ne majalisar dattawan Najeriya ta bayyana shirinta, na bullo da dokar hukuncin kisa kan masu sace jama'a a kasar.

Wannan kudurin ya biyo bayan amincewa da shawarwarin da kwamitin hadin gwiwa na majalisar mai kula da harkokin 'yan sanda, tsaro da leken asiri suka gabatar dangane da yadda batun sace mutane da yin garkuwa da su suka sake kunno kai a cikin kasar.

'Yan majalisar sun bayyana cewa, aiwatar da hukuncin kisa kan wadanda suka aikata wannan laifi zai zama izna ga saura.

Don haka suka bukaci gwamnatocin jihohin kasar, da su bullo da dokokin da za su taimaka wajen hukunta wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China