in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Buhari: Najeriya za ta martaba hukuncin da kotun ICJ ta yanke kan yankin Bakassi
2016-05-05 09:26:25 cri
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana cewa, Najeriyar za ta martaba hukuncin da kotun kasa da kasa ta yanke game da yankin Bakassi.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da ya gudanar tare da takwaransa na kasar Kamaru Paul Biya a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Shugaba Bubari ya ce, babu wani dalili na nuna damuwa ko fargaba game da wannan hukunci, kasacewar Najeriya kasa ce mai bin doka kana tana da kima da mutunci a idon duniya.

Sai dai shugaba Buhari ya ce, duk da cewa kasar ta amince da wannan hukunci, amma har yanzu ba a warware batutuwan da suka shafi ruwaye na kasa da kasa ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China