Mr. Soro, wanda ya yi wannan kira a birnin Abidjan, yayin taron 'yan majalissun dokokin Afirka da na kasashen larabawa, ya ce akwai bukatar hadin gwiwa da goyon bayan juna, tare da kara jan hankalin dukkanin masu ruwa da tsaki, wajen tabbatar da nasarar wannan buri.
Ya ce musayar bayanai da kwarewa, da kuma samar da isassun kayan aikin da ake bukata, na sahun gaba wajen tabbatar da nasarar yaki da ayyukan ta'addanci.
Dandalin 'yan majalissun kasashen Afirka da na kasashen Larabawa na da nufin hada bangarorin 'yan majalissun sassan biyu, domin tattauna batutuwa da suka jibanci yankunan su cikin hadin gwiwa.(Saminu Alhassan)