in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi maraba da yadda kwamitin sulhu na MDD ya soke takunkumin da ya kakkaba wa kasar Cote d'Ivoire
2016-04-29 20:44:35 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kasar Sin ta yi maraba da yadda kwamitin sulhu na MDD ya soke takunkumin da ya kakkaba wa kasar Cote d'Ivoire, kuma a cewarsa hakan na da muhimmiyar ma'ana sosai.

Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri a wannan rana cewa, za a soke takunkumin da aka kakkaba wa kasar Cote d'Ivoire a fannonin hana jigilar makamai da sauransu da aka sanya mata tun a shekarar 2004.

Mr. Liu Jieyi ya bayyana cewa, soke takunkumin da aka kakkaba wa kasar Cote d'Ivoire ya shaida cewa, kasashen duniya sun ganmsu da yunkurin shimfida zaman lafiya da kuma ci gaban da aka samu a kasar ta Cote d'Ivoire, lamarin na zama abin koyi ga kwamitin sulhu na MDD wajen daidaita muhimman batutuwa da suka shafi kasashen Afrika. A halin yanzu, kwamitin sulhu na MDD na ci gaba da sanya takunkumi kan wasu kasashen Afrika, kasar Sin tana fatan wadannan kasashe za su yi kokari tare da sauran kasashen duniya wajen sassauta lamura da inganta yunkurin shimfida zaman lafiya, domin farfado da bunkasuwarsu ta yadda za a cire takunkumin da aka kakaba musu.

Yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Cote d'Ivoire a shekarar 2002 ya yi sanadiyar rikici a kasar. Sabo da haka, kwamitin sulhu na MDD ya fara sanya mata takunkumi a fannonin hana jigilar makamai da hana wasu jami'an kasar yin tafiye-tafiye da sauransu tun daga watan Nuwamba na shekarar 2004.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China