Pellegrini wanda zai mika aiki ga Pep Guardiola a kakar wasa mai zuwa, ya ce nasarar da kungiyar Leicester City ta samu a wannan karo abun ne da ya faru bisa dama da sa'a, kuma ba ya ganin cewa kungiyar za ta iya kiyaye wannan matsayi, domin ba ta da isashen kudi na cimma wannan buri. Yayin wata zantawa da ya yi da kafar watsa labaru ta El Mundo, Pellegrini ya ce yadda kungiyar Leicester City ta cimma nasara wannan karo ba wani darassi ba ne, domin ana gudanar da al'amuran kungiyar yadda ya kamata, kuma 'yan wasan kungiyar suna cikin koshin lafiyar jiki, ban da kalilan dake da rauni. Sai dai, a cewarsa, kungiyar ba za ta iya kare matsayinta ba cikin shekaru 8 zuwa 10 masu zuwa, domin dukkan manyan kuloflika da ke iya kare kambin su, suna da kudi masu yawa a lalitar su. (Bello Wang)