160505-kungiyar-leicester-city-ta-lashe-kambin-premier-league-bello.m4a
|
Kulob din Leicester City ya samu damar lashe kambin gasar Premier League ta kasar Birtaniya a ranar Litinin, duk da cewa ba a gama dukkannin wasannin kakar wasa ba tukuna. Kungiyar ta cimma nasarar daukar kofin na bana ne bayan da Chelsea daTottenham Hotspur suka tashi kunnen dokin 2 da 2, a wasan su na ranar Litinin a birnin London.
Nasarar da kungiyar Leicester City ta samu a wanna karo ya baiwa mutane mamaki sosai, ganin yadda kungiyar ta kusan rasa damar ci gaba da taka leda a tsarin gasar ta Premier League shekara daya da ta wuce, sakamakon kasa samun nasara a wasanni da dama, amma sai ga shi a bana ta lashe kambin tsarin gasar a karon farko a tarihin kafuwar ta.
A kakar wasa ta bana, kungiyar Leicester City ta yi matukar burge masu sha'awar kwallon kafa, bisa nasarorin da ta samu kan wasu manyan kulofulika masu karfi kamar su Manchester United, Chelsea, da dai makamantansu.
A yayin wasan da ya raba gardamar nasarar gasar Firimiyar ta bana kuwa, wanda kuma ya gudana a daren ranar Litinin a birnin London, kungiyar Spurs na bukatar lashe wasan da ta buga da Chelsea, wanda hakan zai bata damar wuce kungiyar Leicester City da yawan maki. Kuma har zuwa lokacin hutun rabin lokaci, Spurs din na da kwallaye 2, yayin da Chelsea ke nema. Amma daga bisani Chelsea ta farke kwallaye 2 da aka zura mata a raga, lamarin da ya tabbatar da matsayin Leicester City wadda ta lashe gasar firimiyar ta bana.(Bello Wang)