in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Zimbabwei za ta sayar da takardun bashi da darajarsu don sasauta matsalar karancin tsabar kudi
2016-05-06 11:49:45 cri

A wani taron manema labarun da aka shirya a ran 4 ga watan, Mr. John Mangudya, Gwamnan babban bankin kasar Zimbabwei ya sanar da cewa, kasar za ta sayar da takardun basusukan da darajarsu za ta kai dalar Amurka miliyan dari 2 nan da kwanaki masu zuwa, sannan za ta rage adadin kudin da za a rika cirewa daga banki, da yawan dalar Amurka da za a fitar da su kasashen waje domin kokarin sassauta matsalar karancin dalar Amurka da ake fama da shi a kasar.

Gwamnan babban bankin kasar ya sanar da cewa, takardun basusukan da babban bankin kasar Zimbabwe zai fitar, su ne na takardun kudi, kamar ta dala 20, dala 10, da dala 5 da dala 2, wadda darajarsu ta yi daidai da dalar Amurka. Bankin shigi da fici na Afirka ne zai ba da lamuni ga babban bankin kasar Zimbabwe a lokacin da gwamnatin kasar take fitar da wadannan takardun bashi,

Mr. John Mangudya ya nuna cewa, "sayar da takardun bashi ba wata hanya ce ta sake yin amfani da dalar Zimbabwe ba. Tun bayan da aka yi watsi da dalar Zimbabwe a shekarar 2008, dalar Zimbabwe ba ta da wani amfani."

Mr. Mangudya ya kara da cewa, babban bankin kasar ya taba nazarin hanyar shigar da kudaden waje iri iri a kasar domin sassauta halin da ake ciki ta fuskar tattalin arziki, amma yanzu 'yan kasar sun fi son yin amfani da dalar Amurka kawai. Sakamakon haka, bankunan wurin suke fuskantar matsin lamba sosai. Yanzu ya zama wajibi a koma tsarin yin amfani da kudaden waje iri iri a kasar, ta yadda za a daidaita matsalar karancin kudi da kuma farfado da tattalin arziki.

Tun daga jiya Alhamis, babban bankin Zimbabwe zai yi musayar wasu kudin da kasar za ta samu domin fitar da kayayyaki da hidima ga kasashen waje, wato yawan kudin Rand zai kai kashi 40 cikin kashi dari, sannan yawan Euro zai kai kashi 10 cikin kashi dari. A watan Janairu na bana, Mr. Mangudya ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Zimbabwe ta amince a yi amfani da kudaden dalar Amurka, da Rand ta kasar Afirka ta kudu, da kudin Euro da fam na Burtaniya da kudin Yuan na kasar Sin da kuma Yuen na Japan, amma ya zuwa yanzu 'yan kasar sun fi kaunar yin amfani da dalar Amurka.

A shekarar 2009, tattalin arzikin kasar Zimbabwe ya tabarbare fiye da kima, har ma ta taba fitar da takardar kudi ta dalar Zimbabwe biliyan dubu 10. Wannan ya sa babu wata mafita illa, babban bankin kasar ya yi watsi da dalar Zimbabwe, a kuma fara yin amfani da dalar Amurka da sauran kudaden waje a kasar Zimbabwe domin ceto tattalin arzikin kasar. A hakika dai, yanzu haka jama'ar kasar sun fi son yin amfani da dalar Amurka da kuma Rand kalilan a kasuwannin kasar Zimbabwe. Amma bayan da darajar Rand ta kasar Afirka ta kudu ta ragu sosai, yawancin 'yan kasuwa sun ki karbar kudin Rand.

Bayan da aka shiga sabuwar shekarar 2016, kasar Zimbabwe ta fada matsalar karancin kudi. Mr. Mangudya ya bayyana cewa, dalilin da ya sa ake fuskantar matsalar kudi a kasar shi ne, gibin cinikin waje da karuwar darajar dalar Amurka tare da raguwar farashin muhimman kayayyaki a kasuwannin duniya.

Yanzu, babban bankin kasar Zimbabwe ya bukaci duk masu aikin ba da hidima da su sanya na'urorin cinikayya na zamani wato POS a shagunansu, kuma ya nemi jama'a da hukumomi daban-daban kamar 'yan kasuwa, da kamfanoni da kananan hukumomi da na more rayuwar jama'a da makarantu da tasoshin sayar da man fetur da su yi amfani da katin banki a lokacin da suke cinikayya domin rage yawan kudin da ke kewayawa a hannun jama'a.

A waje daya kuma, babban bankin kasar ya kayyade yawan dalar Amurka da za a cire daga injin banki, wato kowane mutum yana iya cire dalar Amurka dubu 1, ko Euro dubu 1 ko Rand dubu 2 a kowace rana. Sannan duk wanda zai bar kasar Zimbabwe zai iya fita da dalar Amurka dubu 1 ne kawai, ba dalar Amurka dubu 5 ba kamar yadda aka saba a baya.

Daga karshe, Mr. Mangudya ya bayyana cewa, ana bukatar dogon lokaci kafin wadannan sabbin matakai su taka rawar farfado da tattalin arzikin kasar Zimbabwe. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China