in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi wa gwamnatin Zimbabwe garan-bawul
2014-12-11 19:16:20 cri

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya gudanar da gagarumin garan-bawul ga gwamnatinsa, wanda ya haifar da sauke mataimakiyarsa Joice Mujuru da wasu ministoci 7 daga mukamansu.

Shugaba Mugabe wanda a yanzu haka ke da shekaru 90 da haihuwa ya bayyana hakan ne a ranar 9 ga watan nan, kafin daga bisani a ranar 10 ga wata, ya ayyana ministan shari'a Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon babban mataimakinsa, kuma babban mataimakin shugaban jam'iyya Zanu PF mai mulkin kasa. Kaza lika shugaba Mugabe ya nada Phelekezela Mphoko a matsayin mataimakin shugaban kasa na biyu. Matakin da zai sanya Emmerson Mnangagwa din kasance magajin farko ga shugaba Mugabe.

Emmerson Mnangagwa mai shekaru 68, da ake wa lakabi da kada, sabo da jan halinsa, da karfin zuciya, ya kasance daya daga mafiya biyayya ga manufar tattalin arziki ta kishin kasa da shugaba Mugabe ya tsara, yana kuma goyon bayan Mugabe kan manufar mayar da harkokin tattalin arziki zuwa ga 'yan kasa, wadda ta umarci masu zuba jari na kasashen ketare, da su mika a kalla kaso 51 bisa dari na hannayen jarinsu ga 'yan kasa, manufar da ta sha suka daga masu zuba jari na kasashen ketare, ta kuma ba su tsoro.

Sai dai duk da hakan, wasu masana tattalin arziki na ganin cewa, bisa sakamakon da aka samu a kasar, a matsayin ministan kudin kasar cikin shekarun 1990, Mnangagwa ya fi shugaba Mugabe kwarewa a fannin sanin yanayin tattalin arziki, ya kuma kware a fannin samar da daidaito tsakanin bukatun tattalin arzikin kasar da harkokin siyasa.

A shekarun 1960, lokacin yana da shekaru 19 a duniya, an taba daure shi a gidan yari, sakamakon kiyayyarsa ga mulkin mallakar kasar Burtaniya, daga bisani kuma aka yanke masa hukuncin kisa bisa zargin neman kifar da gwamnatin ta wancan lokaci, sai dai ba a zartas da hukuncin ba sabo da shekarunsa ba su kai 21 ba a lokacin. A yayin zamansa a kurkuku ne kuma ya hadu da Robert Mugabe, ya kuma samu amincewarsa. Kaza lika ya taimakawa shugaba Mugabe a fafitikar neman 'yancin kan kasar, bayan fitowarsu daga kurkuku. Har ila yau, bayan da aka kawo karshen yakin neman 'yancin kan kasar a shekarar 1980, Mnangagwa ya rike mukaman ministan tsaro, da shari'a da ma wasu mukamai na majalisar ministocin kasar.

Hakika dai takara tsakanin Emmerson Mnangagwa da korarriyar mataimakiyar shugaban kasar Joice Mujuru ta fara a lokacin neman gadon mukamin shugaban kasa a shekarar 2004, matakin da ya sa aka samu rabuwar kan bangarori biyu cikin jam'iyyar Zanu-PF ta Zimbabwe, bisa bambancin goyon bayan shugabannin biyu.

Ya zuwa babban taron wakilan jam'iyyar na shekarar 2004, Mnangagwa ya riga ya samu galibin goyon baya, na zama babban mataimakin shugaban kasar, amma Mugabe ya nada Joice Mujuru wannan matsayi, domin samar da daidaito a rabon mukamai tsakanin shugabannin kasar maza da mata a cikin gwamantin tasa. A kuma wannan lokaci ne Joice Mujuru ta kuma samu babban goyon baya daga mai gidanta, watau tsohon babban hafsan dakarun kasar, wanda ya rasu a shekarar 2011.

Ana iya cewa yanayin siyasar kasar ta Zimbabwe ya fara sauyawa ne, tun daga watan Oktobar bana, inda uwargidan shugaban kasar Grace Mugabe mai shekaru 49 ta fara zargin Joice Mujuru da laifin neman sauya tsarin siyasar kasar a asirce, tare kuma da aikata cin hanci da rashawa.

Daga bisani kuma, shugaba Mugabe ya rika bayyana Joice Mujuru a matsayin mai kokarin yi masa makarkashi da kokarin hallaka shi, domin ta samu damar darewa mukamin shugabar kasar ta Zimbabwe, zargin da Joice Mujuru ta yi watsi da shi, tana mai jaddada matukar goyon bayanta ga shugaba Mugabe.

A yayin babban taron wakilan jam'iyyar mai mulki karo na shida da ya gudana a ranar 2 zuwa 6 ga watan nan da muke ciki ne kuma, aka ayyana sunan Grace Mugabe a matsayin shugabar gamayyar mata ta jam'yyar Zanu PF, tare da kawar da izinin shigar Joice Mujuru kwamitin tsakiyar jam'iyyar, ita da wasu ministoci 7 masu goyon bayanta. Yayin da kuma shugaba Mugabe ya ci gaba da kasancewa shugaban jam'iyyar, wanda kuma zai mata takara a babban zaben kasar na shekarar 2018.

Bugu da kari, an bayyana cewa shugaba Mugabe zai sanar da sabbin mambobin majalisar ministocinsa, matakin da zai kawo karshen sauye-sauyen da siyasar kasar ke fuskanta.

Da yake tsaokaci game da yanayin da siyasar kasar ta shiga, Mr. Mnangagwa ya ce sauye-sauyen ba za su rage karfin jam'iyyar mai mulkin kasar ba. Ya ce kwaskwarimar wata hanya ce ta musamman, wadda za ta haifar da ci gaba. Mnangagwa ya kara da cewa a halin yanzu, su na cikin wani yanayi ne na gudanar da kwaskwarima, watau lokacin da ya dace a kawar da dukkanin harkokin da za su haddasa illa ga neman hanyar bunkasuwa. Duk da cewa dai wasu na ganin dalilin da ya sa shugaba Mugabe ya zabi Emmerson Mnangagwa a matsayin magajinsa shi ne, amincewar da ya yi cewa Mnangagwa zai iya kiyaye moriyar iyalansa yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China