in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ta fidda sabbin tsabar kudi
2014-12-19 16:16:30 cri

Babban bankin kasar Zimbabwe ya fidda sabbin tsabar kudi da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 10, a kokarin sassauta mawuyacin halin da 'yan kasar ke fuskanta na karancin canji sakamakon rashin tsabar kudin.

Kasar ta Zimbabwe dai ta samar da tsabar kudi na kashin kanta ne, bayan da ta fara amfani da kudin Amurka a shekarar 2009 a madadin kudin kanta, matakin da ya sanya wasu nuna damuwa kan ko za a sake komawa amfani da kudin kasar bayan bayyanar tsabar kudin da aka fitar.

Tun da sanyin safiyar ranar Alhamis 18 ga watan nan na Disamba ne bankuna daban daban a kasar Zimbabwe, suka fara gabatar da sabbin tsabar kudin, wadanda aka fidda a kwabo daya, da kwabo 5, da kwabo 10, da kuma kwabo 25, kana darajarsu ta yi daidai da darajar kudin Amurka.

Ko da yake har ya zuwa yanzu mafiya yawan al'ummar kasar ba su kai ga ganin sabbin tsabar kudi ba, a hannu guda ana sa ran cewa wannan tsabar kudi za su karade sassan kasar. Wani dan kasar Birtaniya mazaunin kasar mai suna Richard, ya bayyana cewa,

"Idan darajarsu ta kai kamar kudin Amurka, hakan zai yi kyau sosai wajen samun canji, sabuwar tsabar kudin ta Zimbabwe ta fi tsohuwar takardar kudi ta Amurka. A da, babban kanti kan ba ni canji da takardar wakilcin kudi da ake iya amfani da su sau da yawa, amma yanzu an fara amfani da sabuwar tsabar kudin Zimbabwe, hakan ya yi kyau, ina farin ciki da hakan sosai!"

A shekarar 2009 da ta gabata, an samu hauhawar farashin kayayyaki mai tsanani a Zimbabwe, wanda hakan ya sa aka fidda takardar kudin Zimbabwe da kowace daya ta kai darajar biliyan 10.

A kokarin farfado da tattalin arzikin kasar ne kuma babban bankin kasar, ya dakatar da amfani da kudin Zimbabwe, aka koma amfani da kudin Amurka, tare da amincewa da amfani da kudin Birtaniya, da na Afirka ta Kudu, da na Botswana, da sauransu a kasar ta Zimbabwe.

Sai dai yayin da aka fara amfani da kudin Amurka a Zimbabwen, ba a shigar da tsabar kudin Amurkan ba. A sabili da haka, farashin kowane irin kaya ya haura zuwa dala daya a kasar, yayin da aka fara fuskantar matsaloli da dama masu alaka da neman canji.

Darektan gudanarwa na cibiyar nazari da bayanai ta kudancin Afirka ya bayyana wa wakilinmu cewa, gabatar da sabuwar tsabar kudin zai rage farashin kayayyaki, tare da warware wannan matsala ta canji, a kokarin sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin kasar. Ya ce,

"A ganina, wannan mataki zai ba da gudummawa ga samun bunkasuwa, sabo da mutane su kan gamu da matsalolin karancin samun canji, a yayin da suke sayayya a manyan kantuna. Ko da yake manyan kantuna su kan fitar da takardar wakilcin kudi, matsalar ita ce ba a kowane babban kanti ake iya amfani da ita ba. Dadin dadawa, sabo da karancin tsabar kudi, farashin kayayyaki ya yi sama sosai. Sabuwar tsabar kudin za ta warware wannan matsala."

Tun bayan da aka daina amfani da kudin Zimbabwe, an ci gaba da amfani ne da tsabar kudin Rand na Afirka ta Kudu, da tsabar kudin Pula na Botswana a kasar idan har ana da bukatar canji. Amma sabo da sauyawar ma'aunin musanya tsakanin kudade, wasu manyan kantuna ba su son amfani da tsabar kudin kasashen waje, wanda hakan ne ya sanya su fara bada canji ta hanyoyi daban daban, inda wasu ke bada takardar wakilcin kudi irin tasu, wasu kuma ke rubuta yawan canjin a takardar rasiti, ta yadda masu sayayya kan iya amfani da canjin a wani karon. Har ma wasu kan baiwa masu sayayyar wasu kayayyaki domin maye gurbin canji, misali, sukan bada alkalamin rubutu kan kwabo 20, yayin da wani cigam akan bada shi kan kwabo 5.

Ko da yake ba a dade da gabatar da sabuwar tsabar kudin ba, duk da haka wasu masu kantuna sun fara nuna damuwarsu, kan ko sabbin kudin za su samu amincewar jama'a ko a'a. A wani babban kanti mai suna Fort Madge dake Zimbabwe, wani mai kula da kanti ya gayawa wakilinmu cewa, an yi latti kwarai wajen gabatar da tsabar kudin. Ya ce,

"Yanzu tsabar kudin Rand ta riga ta samu karbuwa ga jama'a, kuma ana iya amfani da ita a kowane wuri a Zimbabwe. A ganina, da kyar wannan sabuwar tsabar kudi za ta samu karbuwa daga mutane cikin gajeren lokaci."

A kokarin samun karbuwar jama'a, yanzu hukumomin hada hadar kudi na Zimbabwe suna kokarin gabatar da shirin fadakarwa domin wayar da kan jama'a game da amfani da sabuwar tsabar kudin.

Ya zuwa yanzu, ana iya amfani da ita a kasar Zimbabwe ne kawai. Za kuma a ci gaba da mai da hankali kan sakamako da za a samu cikin dogon lokaci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China