in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kula da harkokin inganta fasahohin gida na Zimbabwe ya yi kuskure wajen bayyana manufofin gwamnati
2016-04-25 13:41:45 cri

Ya zuwa yau Litinin 25 ga wata, saura mako daya kacal na wa'adin karshe da gwamnatin kasar Zimbabwe ta tsara na soke takardar kamfanoni masu jarin waje ta yin cinikayya a kasar Zimbabwe, daruruwan kamfanoni masu jarin waje ne kawai suka gabatar da shirin yin kwaskwarima don mayar zama kamfanonin kasar Zimbabwe. Ga alama, mai yiyuwa ne gwamnatin kasar Zimbabwe ba za ta shawo kan kamfanoni masu jarin waje wadanda ba su son mayar da kansu zama kamfanonin kasar. A ranar Jumma'ar makon jiya, wato 22 ga watan, a fili, Mr. Parick Zhuwao, ministan kula da harkokin matasa da inganta fasahohin gida da ba da izinin bunkasa tattalin arziki na kasar Zimbabwe ya amince da cewa, ya yi kuskure wajen bayyana manufofin gwamnati game da mayar da kamfanoni masu jarin waje su zama kamfanonin wurin, don haka ya kamata a yi amfani da jawabin da shugaba Robert Mugabe ya yi game da batun.

A ranar Jumma'ar makon jiya, Mr. Patrick Zhuwao ya shirya wani taron manema labaru na musamman, inda ya bayyana cewa, ya yi kuskure a bayanin da ya yi game da dokar mayar da kamfanoni masu jarin waje na zama kamfanonin kasar. Shugaba Robert Mugabe ya yi bayani game da wannan doka a makonni biyu da suka gabata kamar yadda ake fata.

A ran 22 ga watan Maris da ya gabata, Mr. Patrick Zhuwao ya ayyana wa'adin karshe ga kamfanoni masu jarin waje, cewar dole ne kamfanoni masu jarin waje da suka zuba jarin da ya wuce dalar Amurka dubu dari 5 sun sayar da takardun hannun jarinsu da darajarsu bai kamata ta kasa kashi 51 cikin dari ba zuwa ga baki 'yan kasar Zimbabwe, kuma dole ne kamfanoni masu jarin waje su gabatar da shirin aiwatar da wannan doka kafin 31 ga watan Maris. Idan kuma ba su yi haka ba kafin ranar 31 ga watan Maris ba, gwamnatin ta ba su karin kwanaki 30, wato zuwa karshen watan Afrilu domin kammala wannan aiki. Idan ya zuwa karshen Afrilu ba su iya gabatar da shirinsu ba, to, gwamnatin za ta iya mayar musu da takardunsu na yin cinikayya kai tsaye ba tare da ta sanar musu ba.

Bayanan da Patrick Zhuwao ya yi ya ta da hankalin kamfanoni masu jarin waje dake kasar Zimbabwe. Sakamakon haka, a ran 12 ga wata, shugaba Robert Mugabe ya yi wani bayani na musamman, inda ya ce, a lokacin da ake mayar da kamfanoni masu jarin waje su zama kamfanoni wurin, za a bambanta kamfanoni masu sarrafa albarkatun kasa da wadanda ba sa sarrafa albarkatun kasa da sauran sana'o'i. Muddin a lokacin da ake shirin kafa sabon kamfani mai sarrafa albarkatun kasa mai jarin waje da na gida, dole ne yawan jarin dake hannun baki 'yan kasar Zimbabwe ya kai a kalla kashi 51 cikin dari. Amma sauran kamfanoni masu sarrafa albarkatun kasa da suka shafe shekaru da yawa suna aiki a kasar, idan ba su kai wannan ma'auni ba, amma darajar albarkatun kasa da suka hako ta zauna a cikin kasar ta hanyoyin biyan albashin ma'aikata, da bonas, da haraji da sayen kayayyaki a wurin, za su iya ci gaba da tafiyar da harkokinsu a kasar ta Zimbabwe.

Bugu da kari, shugaba Mugabe ya kayyade ikon ma'aikatar kula da harkokin matasa da inganta fasahohin gida da ba da izinin bunkasa tattalin arziki ta kasar, wato bayan da aka zartas da manufofin inganta fasahohin gida a majalisar ministocin gwamnati, ma'aikatar za ta shugabanci aiki, kuma ta dauki nauyin daidaita harkokin dake shafar hukumomin gwamnati daban daban.

Tun daga shekarar bara, tattalin arzikin kasar Zimbabwe ya shiga cikin mawuyacin hali, lamarin da ya sa kamfanonin wurin ke kasa samun kudi. Bugu da kari, sakamakon bala'in farin da ake fuskanta a kasar, kasar tana cikin halin karancin abinci, yanzu yawan 'yan kasar da suke fama da yunwa ya kai sulusi, kuma jama'a na dogara da kayayyakin da aka shigo da su daga ketare da taimakon da aka ba su. Masanan nazarin ilmin tattalin arzikin wurin suna ganin cewa, a irin wannan yanayin da ake ciki, idan aka ci gaba da aiwatar da manufofin mayar da kamfanoni masu jarin waje su zama kamfanonin wurin, tabbas ne za a kara yi wa tattalin arzikin kasar Zimbabwe illa. A lokacin da Patrick Zhuwao ya ce, za a fara aiwatar da wannan manufa a bankuna masu jarin waje, an samu karancin tsabar kudi a bankunan kasar.

Yanzu gwamnatin kasar Zimbabwe ta fara sassauta matsayinta kan manufar inganta fasahohin gida a kokarin kawar da alamun gurgunta tattalin arzikin kasar da kuma sa kaimi ga jarin waje. Bisa halin da ake ciki yanzu, dole ne kamfanoni masu sarrafa albarkatun kasa da ke kasar su martaba manufar mayar da su kamfanonin wurin, kana gwamnati tana sassauta matsayinta kan sauran sana'o'i. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China