in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimbabwe ya gabatar da bayanai da suka shafi kasar tun bayan shekaru 8
2015-08-26 14:53:52 cri

A ranar 25 ga watan nan ne shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya gabatar da bayani game da yanayin da kasar ke ciki a majalisar dokokin kasar. Bayanin kuwa ya zama irinsa na farko da shugaba Mugabe ya gabatar tun bayan shekaru 8 da suka wuce. Cikin jawabin nasa, Mista Mugabe ya sa kaimi game da muhimmancin zuba jari a kasar da ma kasashen ketare, sai kuma batu game da gyara masana'antun gwamnatin kasar. Haka zalika bayanan nasa sun tabo batun karfafa dangantaka a tsakanin kasar da kasashen yammacin duniya, wadda ta yi tsami har na tsawon sama da shekaru 10, inda karon farko ne aka ambaci yadda za'a samar da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasar da kasashen yammacin duniyar.

Robert Mugabe mai shekaru 91 ya ce, yana maraba da kasashen yammacin duniya da su zuba jari a kasar Zimbabwe da nufin raya tattalin arzikinta, kana yana da aniyar inganta hadin gwiwa tare da wasu hukumomin duniya, musamman ma hukumar ba da lamuni ta duniya wato IMF da kuma bankin duniya.

A sa'i guda kuma, Mugabe ya jaddada cewa, Zimbabwe ta samu nasarar farfado da tattalin arzikinta ne sakamakon taimakon da kasar Sin ta bayar, kuma gwamnatin kasar ta daddale yarjejeniyoyi a wasu fannonin da suka shafi makamashi, sadarwa, ayyukan noma, ma'adinai da yawon bude ido. Mugabe ya kuma yaba wa kudin rance da yawansu ya kai dalar Amurka sama da miliyan 90 da Sin ta bayar don sayen kayayyakin aikin kiwon lafiya.

Mugabe ya ce, gwamnatinsa ta fara yin gyare-gyare ga masana'antun kasar, don kyautata aikin samar da kayayyaki, gami da samar da kyakkyawan yanayi wajen gudanar da harkokin kasuwanci.

Bugu da kari, Mugabe ya ce, watakila yanayin bunkasar tattalin arzikin kasar zai tsaya ne a kashi 1.5 cikin 100 a bana, sabanin kashi 3.5 cikin 100 kamar yadda aka yi hasashe a farkon shekarar, kuma dalilin da ya sa aka samu tafiyar hawainiyar bunkasuwar tattalin arziki shi ne, sabo da yanayin fari ya kawo raguwar yawan hatsi. Nan gaba, gwamnatin Mugabe za ta himmatu wajen farfado da aikin gona ciki har da auduga da sauransu, da fadada sana'ar hakar ma'adinai. Kazalika za a kafa yankunan musamman na tattalin arziki, da kara azama ga kananan da matsakaitan masana'antun kasar, a kokarin kara karfafa zukatan jama'a a kan hukumomin kudin kasar.

Ban da wannan kuma, bisa dokar da babbar kotun kasar ta bayar a ranar 17 ga watan Yuli, gwamnatin kasar za ta sake yin bincike kan dokar 'yan kwadago ta kasar, don soke wasu ka'idoji marasa adalci da aka tanada a ciki kan cewa, shugaban kamfani na da ikon kore ma'aikatansa ba tare da biya diyya ba. Mugabe ya ce, burin da ake kokarin cimmawa shi ne a samu moriyar juna.

Bugu da kari, gwamnatin kasar za ta zuba jari da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 125 wajen harkokin sadarwa, don gaggauta raya gidajen rediyo da talebiji ta hanyar zamani, gami da kafa cibiyoyin ba da aikin jinya 53 a kauyuka don kyautata matsayin kiwon lafiyar jama'a.

Bayan da kasashen yammacin duniya suka kakaba takunkumi ga Zimbabwe har na tsawon shekaru 12, 'yan kasuwar kasashen waje sun janye jarin da suka zuba a kasar, sa'annan sun kaurar da masana'antunsu zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita. Don haka yanzu, Zimbabwe na bukatar jarin ketare cikin gaggawa domin sa kaimi ga raya tattalin arzikinta. A karshen shekarar bara, kungiyar EU ta sanar da soke takunkumin da ta saka wa Zimbabwe, kuma ta yi shirin ba da kudin taimako da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 300 daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2020. Haka kuma bankin duniya ya kafa wani asusun sake farfado da Zimbabwe, asusun IMF shi ma yana binciken yanayin da ake ciki a kasar. Manazarta sun nuna cewa, dalilin da ya sa Mugabe ya yi wannan bayani shi ne don nuna sahihancinsa kan maido da hadin gwiwa tare da kasashen yammacin duniya. A halin yanzu, yanayin zuba jari a Zimbabwe yana samun kyautatuwa, ko shakka babu za ta samu farfadowar tattalin arzikinta, muddin akwai kyawawan manufofin zuba jari.

Amma, bayanin da shugaba Mugabe ya bayar ya samu shakku daga wasu 'yan majalisa daga jam'iyyar adawa ta kasar, wadanda suke ganin cewa, shugaba Mugabe bai kawo hanyar da za a bi wajen samar da guraben aikin yi ba. Haka kuma, wasu manazarta sun ce, duk da cewa, Mugabe yana maraba da jawo jari daga kasashen waje, amma bai dauki matakan kawar da kalubalen da ke kawo cikas ba ga aikin, wadanda suka hada da aikin yin wa yankunan kasar kwaskwrima da kuma ba da kariya a harkar cinikayya. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China