in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayin gasannin NPFL na Najeriya: Pillars ta lashe Sunshine, Nasarawa ta lashe Wolves
2016-05-05 18:56:08 cri
Adamu Mohammed na kulob din Kano Pillars wanda ke cikin 'yan wasa masu jiran canji, ya shiga filin wasa a minti na 82 bayan fara wasa tsakanin Pillars da Sunshine Stars a ranar Lahadi, ya kuma ci wa Pillars kwallo daya wadda ta tabbatar da nasarar kulob din kan Sunshine Stars.

A nasu bangaren, kwallaye 2 da Esosa Igbinoba ya ci, su suka tabbatarwa Nasarawa United nasarar tashi da maki 3 kan Warri Wolves. Nasarawa United dai ta doke Warri Wolves, da ci 2 da nema ne a filin wasa na Aper Aku dake birnin Makurdin jihar Benue.

A nasa bangare, kulob din dake kan gaba a teburin tsarin gasar NPFL wato Enugu Rangers ya kwashi rashin nasara a hannun Rivers United da ci 3 da 1, a wasan da suka buga a birnin Port Harcourt. A bangaren 'yan wasan Rivers United wadanda suka taka rawar gani yayin wasan, inda Bernard Ovoke ya ciwa kungiyar ta sa kwallaye 2 a minti na 17 da na 45 bayan fara wasa, kana Christian Weli shi ma ya zura kwallo daya a raga a miti na 21. Kana a daya bangaren Gabriel Olalekan ya ci gidan su a minti na 47, amma hakan bai taimakawa kungiyar Rangers kare kanta daga yanayin da ta fada ba.

A birnin Ibadan, Shooting Stars ta samu damar yin kunnen doki da Plateau United da ci 2 da 2, sakamakon da ya gamsar da su ta la'akari da yadda Kano Pillars ya lashe Shooting Stars da ci 6 ba ko daya a makon da ya gabata. Yayin da a nasu bangare, Enyimba ta buga kunnen doki da Lobi Stars da ci 2 da 2 a filin wasan Enyimba dake Aba na jihar Abia. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China