Ya kuma fara aiwatar da wannan kuduri na sa ne lokacin da aka maida shi aiki zuwa birnin Nairobi shekaru 8 bayan kasancewar sa a Wajir. A kuma wannan lokaci ne ya bukaci a dauke masa aikin dan sanda na yau da kullum, domin ya maida hankali ga horasa da 'yan wasan motsa jiki musamman masu wasanni na gudu.
Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Samson Katam ya ce shi kan sa ya taba lashe gasar gudun mita 1,500. Ya kuma wakilci hukumar 'yan sandan kasar Kenya a gasanni da dama, lokacin da hukumar 'yan sandan ba ta cikin sashen masu wakiltar kasar a harkokin wasanni.
Samson Katam ya ce ya samu horo a kwalejin Malezi dake Nairobi a shekarar 2006. Ya kuma samu takardar shaidar Difloma a jami'ar Moi. Daga bisani kuma an damka masa aikin horas da 'yan wasan hukumar 'yan sanda ta AP.
Ya ce a shekarar 2008, an hade sashen wasanni na hukumar 'yan sandan Kenya, da babbar hukumar harkokin wasanni ta kasar, wanda hakan ya bude wata babbar dama da a baya basu samu irin ta ba.
Katam ya ce ya horas da manyan 'yan wasa sama da 30, ciki hadda tsaffin zakarun gudun yada-kanin wani 'yan kasar Kenya Patrick Makau, da Abel Kirui. Ya kuma samu daukaka mai tarin yawa a fannin wasannin motsa jiki, fannin da tun da jimawa yake sha'awar yin fice a cikin sa.(Saminu Alhassan)