in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fiye da mutane dubu 100 suke ratsawa ta Nijar a kowace shekara
2016-05-05 10:10:41 cri
Hanyar da ta zama dole ga mutanen kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara domin neman zuwa Turai, kasar Nijar ta kiyasta mutane fiye da dubu 100 dake ratsa kasar a kowace shekara, in ji ministan harkokin wajen Nijar, Ibrahim Yacouba.

Shugaban diplomasiyyar Nijar ya bayyana hakan a yayin wata ganawar aiki tare da ministocin harkokin wajen kasashen Faransa da Jamus, Jean-Marc Ayrault da Frank-Walker Steinmeier, da suka kai wata ziyarar aiki a Nijar a ranar Talata.

Shugabannin diplomasiyyar kasashen Faransa da Jamus sun je Nijar domin tattaunawa tare da manyan hukumomin kasar kan batun tsaro a yankin Sahel da kuma musamman ma babbar matsalar kwararar bakin haure.

Domin yaki da bakin haure ba bisa doka ba, ya kamata a yi yaki da dalilan da suka haddasa rashin tsaro, talauci, raunin demokaradiyya a cikin wasu kasashe, da kuma sauyin yanayi, in ji mista Yacouba.

A kasar Nijar, gwamnati ta amince da wani tsari na kudin Euro biliyan daya wanda a cikinsa kasar take bukatar taimakon gamayyar kasa da kasa, musammun ma kungiyar tarayyar Turai domin samar da kudaden gudanar da wadannan ayyukan da za su taimaka wa wajen warware matsalolin da suka zama tushe na hijira ba bisa doka ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China