in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaki ya canza rayuwar 'yan gudun hijira na Syria
2016-05-04 13:07:03 cri

Mutane sama da miliyan daya suke gudun hijira sakamakon yakin basasa da ya barke yau da kusan sama da shekaru 5 suka gabata a Syria, lamarin da ya kawo sauyi ga rayuwarsu baki daya. A wani sansanin 'yan gudun hijira na Za'atari dake arewacin Jordan, 'yan gudun hijira na Syria, musamman yara, suna rayuwa da ta sha da bamban sosai da kafin barkewar wannan rikici. 

Ko da yake shekaru uku sun riga sun wuce, amma Umm Khaled ta tuna da lokacin da ta tsere daga Syria zuwa Jordon sosai, ta ce,

"Mun tashi zuwa wani wurin dake iyakar kasar Iraki, daga bisani mun isa Jordan. Mun rada wa wannan hanya mai suna 'Mutuwa', sabo da akwai wahala sosai. Muna neman tsira, amma kome da kome na kasancewa barazanar ga rayukanmu duka. Ana yake-yake, har ma ana ganin harsashi a ko ina. An kai harin jirgin sama sau da dama, mutane da yawa sun mutu a kan hanya."

Yake-yake sun haifar da matsalolin ga tunanin 'yan gudun hijira. Jami'in hukumar UNHCR mai kula da mu'amala da sansanin Za'atari, mista Gavin David White ya furta cewa, dole ne a daidaita wadannan matsalolin dake shafar tunani. Ya ce.

"Kowane mutumin da ya tsira daga Syria, ya ji rauni sosai a zuciya, wanda ke da alaka da irin matsalolin da ya gamu da su, kamar yake yake, da wahalhalun da ya sha a yayin gudun hijira da sauransu. Lokacin da suka isa sansanin, ba su sami sauki daga irin wannan yanayi ba. Shi ya sa yin hira da su domin taimakawa ya zama wani kashi daga cikin ayyukanmu."

Kawo yanzu dai, a cikin 'yan gudun hijira kimanin dubu 80 dake zama a sansanin Za'atari, kashi 57 cikin dari matasa ne. A cikinsu kuma, kimanin kashi 20 cikin dari shekarunsu na kasa da 5 a duniya. Yake yake sun janyo babbar illa ga tunaninsu.

Umm Khaled ta bayyana cewa, mafi yawan yara suna fama da matsalar tunani, ba su saba da yanayin yake-yake da kuma sabon wurin kwana ba. Ta ce,

"Ba su ga abin da ya faru ba, ba su iya sabawa da sabon tsarin tarbiyya ba, shi ya sa ba su son zuwa karatu."

'Yar wanta Isra ta yi kamar haka, wannan yarinya mai shekaru 15 da haihuwa ta yi zama a sansanin Za'atari har na tsawon shekaru biyu. Ko da yake akwai makarantu 9 a nan, amma ta janye jikinta daga karatu. Isra ta ce,

"Na taba zuwa makaranta na aji 8, amma akwai bambanci sosai tsakanin tsarin tarbiya a nan da na Syria. Ba na son shi ko kadan, shi ya sa ba zan je karatu ba. Ina fatan za a tabbatar da zaman lafiya a Syria, sabo da ina son koma wa gida. Daga bisani zan ci gaba da karatu a Syria. Ina fatan zan zama wata malama a nan gaba. Kuma na yi imani, zan koma gida nan ba da dadewa ba."

Kawo yanzu, yara kashi 2 bisa 3 a sansanin suna karatu a makarantu, amma iyayensu na damuwa kan ingancin tarbiya. Ahmed Ali mai shekaru 55 a duniya ya bayyana cewa, 

"Ba a amince da makarantu a nan ba. Da ma yaranmu sun sami maki mai kyau a makarantu, amma yanzu ba mu iya ba su damar samun karatu mai inganci ba."

Muhammad Ramadan na da yara guda uku, a cikinsu yaro mafi girma yana da shekaru 5 da rabi da haihuwa kawai. Ramadan ya ce,

"Suna zama ba tare da dangoginsu ba, ba su san kakaninsu ba, sai dai baba da mama kawai. An katse mu'amalar dake tsakaninsu da sauran membobin iyalinmu."

Game da wadannan yara da aka haifa ko kuma girma a cikin sansanin Za'atari, wannan ne duniyarsu baki daya. Garinsu dake kasar Syria na da nisa kwarai. Wata mutumiyar waje da ta kawo ziyara a sansanin ta tabo wata hira tsakaninta da wani karamin yaro na Syria cewa,

"Na tambaye shi, ka zo daga ina ne? Ya ce, Syria. Sai na sake tambaya cewarsa, don me kana nan? Ya amsa, ban sani ba." (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China