in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta kara karfin kai hari ga 'yan ta'addancin dake Syria
2015-11-18 13:37:27 cri

Kwanaki 16 bayan faduwar jirgin saman kasar Rasha mai dauke da mutane 224 a yankin Sinai na kasar Masar, hukumar tsaron kasar ta Rasha ta tabbatar da cewar 'yan ta'adda ne suka harbo jirgin.

Bayan da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya dawo gida daga taron G20, nan da nan ya kira taron gaggawa don sauraron rahoton da shugaban hukumar kwantar da kura ta kasar Rasha Alexander Bortnikov ya gabatar dangane da musababbin faduwar jirgin saman kasar a yankin Sinai na kasar Masar, inda Bortnikov ya ce, bayan da aka yi bincike kan tarkacen jirgin, da kayayyakin fasinjoji, an gano alamun fashewar wasu sinadarai a cikin jirgin, a cewarsa,

"Muna ganin cewa, an ta da wata nakiyar da karfinta ya kai kilo 1 na sinadaran TNT a cikin jirgin, abin da ya haddasa wargajewar jirgin a sama, sa'an nan tarkacen jirgin suka fado har ma suka watsu cikin wani yanki mai girma. Muna iya tabbatar da cewa, harin ta'addanci ne."

Bayan da ya saurari bayanan shugaban hukumar kwantar da kura ta kasar, shugaba Putin ya yi shiru, sa'an nan ya bukaci dukkan mahalarta taron da su tashi tsaye don girmama wadanda hadarin ya rutsa da su. Cikin jawabin da ya gabatar daga bisani, shugaban ya ce za a bi 'yan ta'adda da suka aikata wannan mummunan aiki duk inda suka boya, don yanke musu hukunci mai tsanani. Shugaban ya ce,

"Ya kamata mu dauki mataki nan take, don gano sunayen wadannan mutane. Duk inda suka boya, za mu yi kokarin gano su. Za mu bi su duk lungun da suka shiga a duniya don a kama su, a kuma yanke musu hukunci. Kasar Rasha za ta tsaya kan doka ta 51 na kundin MDD don gudanar da aikin kama masu laifi. Sa'an nan duk wanda yake son taimakawa masu laifi, ya kamata su san cewa, ba za su yi galaba ba."

Har ila yau, shugaban ya ce jiragen saman yakin kasarsa za su kara karfin hare-haren da suke kai wa sansanonin 'yan ta'adda dake kasar Syria, don sanar da su cewa, dole ne a yanke musu hukunci. Ya ce,

"Ba kawai za mu ci gaba da daukar matakan soja a kasar Syria ba, har ma za mu karfafa hare-haren da muke kaiwa a halin yanzu. Don sanya 'yan ta'adda su fahimci cewa ba zai yiwu su kaucewa hukuncin da za a yanke musu ba. Yanzu ina bukatar ma'aikatar tsaro da hedkwatar rundunar sojoji da su mika shawarwarinsu. Haka kuma zan ci gaba da sanya ido kan yadda ake gudanar da wannan aikin."

A yammacin ranar Talata bisa agogon Rasha ne, shugaba Putin ya je wajen cibiyar ba da umarni ga aikin tsaron kasar Rasha, don sauraron rahotannin da aka gabatar dangane da matakan sojan da ake dauka a kasar Syria. Inda Sergey Shoigu, ministan tsaron kasar Rasha ya bayyana wa shugaban cewa, sojojin sama na kai jerin hare-hare sosai kan ayyukan IS dake kasar Sham.

"An ninka lokutan tashin jiragen sama a ko wace rana, don tabbatar cewa ana kai hare-hare masu karfi kan sansanonin 'yan kungiyar IS dake kasar Sham. Ban da haka kuma wasu manyan jiragen sama masu jefa boma-bomai, wadanda suka tashi daga Hmeimin na kasar Syria ko kuma daga kasar Rasha, su ma sun shiga shirin kai hare-haren da ake yi."

A nasa bangare, babban hafsan hafsoshin sojojin Rasha Valeriy Gerasimov, ya yi tsokacin cewa, bayan da sojojin Rasha suka fara kai hare-hare kan 'yan kungiyar IS a kasar Syria wasu kwanaki 48 da suka wuce, ya zuwa yanzu, jiragen saman yaki na Rasha sun tashi har karo 2289, sa'an nan sun kai hare-hare ko jefa boma-bomai kan sansanoni da ayyukan kungiyar IS har sau 4111, inda aka rushe cibiyoyin ba da umarni na kunigyar guda 562, sansanonin horaswa 64, gami da wuraren kera makamai 54. A cewar babban hafsan,

"A kokarin da muke yi na sauke nauyin dake bisa wuyanmu na kara kokarin kai hare-hare daga sama, mun tsara shirin cewa, za a kara yawan tashin jirgi daga cibiyar sojojin sama dake Hmeimin. Haka zalika, za mu kara tura wasu manyan jiragen saman yaki zuwa kasar Syria."

Bugu da kari a wajen taron, shugaba Putin ya bukaci sojojin kasarsa da su tsara shirin daukar matakan soja na hadin gwiwa tare da sojojin teku na kasar Faransa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China