in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Obama na kokarin neman goyon baya kan daukar matakan soja ga Syria
2013-09-09 17:33:50 cri

A ranar 9 ga wata, majalisar dokokin kasar Amurka za ta kawo karshen hutunta na tsawon mako guda, kuma 'yan majalisar dattawa da ta wakilai gaba dayansu za su koma wurin aiki, inda abin da aka sanya a gabansu shi ne tattauna ko za a danka wa gwamnati ikon daukar matakan soja kan Syria. Duk da haka, ikirarin da aka yi a kwanan baya na nuna rashin amincewa da kuma rashin goyon baya daga gamayyar kasa da kasa duk sun janyo rashin tabbas kan matakan soja da ake son dauka.

Kididdigar da kafar CNN ta bayar ta yi nuni da cewa, daga 'yan majalisar dattawa 100, akwai 25 da suka nuna goyon bayansu, a yayin da wasu 20 suke kan matsayi na kin yarda. Har wa yau, a majalisar wakilai da ke da kujeru 435, 'yan majalisar 24 ne kawai suka nuna goyon baya, a yayin da wasu sama da 123 suka nuna rashin amincewa.

In an yi bincike, za a gano cewa, yadda shugaba Obama da sakataren harkokin waje nasa John Kerry sun kasa cimma burinsu a kokarin da suka yi na neman goyon baya daga kasa da kasa ne ya yi sanadiyyar halin da ake fuskanta yanzu. A taron kolin G20 da aka yi kwanan baya, ba a cimma samar da wata hadaddiyar sanarwa a kan batun ba, kuma ko da kungiyar tarayyar Turai ta yi Allah wadai da yadda aka yi amfani da makamai masu guba, amma cewa ta yi ko za ta dauki matakan soja ko ba za ta yi ba ba zai tabbata ba sai bayan da aka fitar da sakamakon bincike. Duk da haka, abin lura shi ne, yawan wadanda ba su bayyana matsayinsu a majalisu biyu ba sun kai fiye da rabi, don haka, yanzu da wuya a yi hasashen sakamakon kuri'un da za su jefa a wannan mako.

Don lallashin jama'ar kasar Amurka da 'yan majalisa na kasar, ana sa ran cewa shugaba Obama zai tattauna a yau litinin tara ga wata da dare tare da 'yan jarida na wasu manyan gidajen talabijin guda shida na kasar, inda zai bayyana muhimmancin daukar matakan soja kan Syria, haka kuma zai yi alkawarin kayyade tsawon lokaci na matakin soja da yake son dauka. Sannan kuma a ranar 10 ga wata, Obama zai yi wani jawabi ga al'ummar kasar baki daya ta gidan talabijin. Ban da wannan, shugaba Obama tare da mataimakinsa Joe Biden za su tattauna da wasu 'yan majalisa don lallashinsu.

Har wa yau, a ranar 7 ga wata, Mr.John Kerry sakataren harkokin waje na kasar Amurka ya isa birnin Paris a wata ziyarar da ya kai kasar Faransa, inda ya samu goyon baya daga gwamnatin kasar. Dangane da matsalar Syria, gwamnatin kasar Faransa tana kan wani matsayi na hukunta gwamnatin Syria bisa yin amfani da makamai masu guba da ta yi, kuma a ganinta, hakan nan za a iya daidaita matsalar Syria a siyasance, sai dai a cewar gwamnatin Faransa, za ta jira har zuwa lokacin da masanan MDD kan makamai masu guba suka fitar da rahoton bincike, kuma ba za ta dauki matakan soja ba tare da hadin kan Amurka ba. Baya ga haka, tana fatan ganin a daidaita matsalar ta hanyar siyasa.

Ban da haka, a ranar 8 ga wata da yamma, John Kerry ya kuma yi shawarwari da wasu ministocin harkokin waje na kawancen kasashen Larabawa a ofishin jakadancin kasar Amurka da ke Faransa, inda ya yi kira gare su dasu shiga aikin soja kan Syria. Ministan harkokin waje na kasar Qatar da ya halarci shawarwarin ya bayyana cewa, Qatar na nuna goyon baya ga hadaddiyar sanarwar da wasu kasashe 12 na kungiyar G20 suka bayar, sai dai yanzu haka Qatar na nazarin yadda za ta ba da taimako ga jama'ar Syria. A cewar Kerry, gwamnatocin kungiyar tarayyar kasashen Larabawa za su yanke shawara kan ko za su yarda da daukar matakan soja kan Syria ko a'a nan da awowi 24 masu zuwa.

Duk da rashin tabbas da ake fuskanta dangane da ko majalisar dokokin kasar Amurka za ta ba wa gwamnati ikon daukar matakan soja, masana suna ganin cewa, ko majalisar ta yarda ko ba ta yarda ba, gwamnatin Amurka za ta dauki matakan soja, magana ce da ta shafi lokaci ne kawai. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China