in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu tsoffi da kuma sabbin matsaloli na kunno kai a kasar Syria
2013-12-23 17:59:53 cri

Shekarar 2013 da ke dab da karewa ta kasance shekara ta uku da kasar Syria ta shafe tana fama da tashin hankali, inda rikice-rikice ke kara tsananta, kuma ban da matsalolin da kasar ke fuskanta a baya, wasu sabbin matsalolin da suka taso yanzu haka sun fara addabar wannan kasa, wadanda kuma suke kawo rashin tabbas kan makomar kasar. Abokiyar aikinmu Lubabatu na da karin bayani.

A taron manema labarai da aka shirya a ranar 16 ga wannan wata, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, " a shekarar 2013, tsanancewar rikici a kasar Syria ya wuce yadda ake zato, al'ummar kasar ba za su iya ci gaba da hakuri da tashin hankali da barna dake faruwa a cikin wata karin shekara ko wata ko kuma rana ba." Kamar yadda babban sakataren ya fada, a shekarar 2013 da ke dab da karewa, fada ya kara rincabewa a tsakanin sojojin gwamnatin Syria da 'yan tawayen kasar. Tun daga watan Afrilu, sojojin gwamnati suka fara daukar matakai kan 'yan tawaye, kuma daga wancan lokaci, sun fara kwato garuruwan al-Quasyr da Khalidia daga hannun 'yan tawayen. Duk da haka, har zuwa yanzu, sassan biyu na ci gaba da gwabza kazamin fada a garuruwan Homs da Daraa da Aleppo da sauran muhimman wurare. A sa'i daya kuma, yadda wasu kasashen ke yunkurin hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad da kuma wasu dakaru masu tsattsauran ra'ayi da ke da alaka da kungiyar al-Qaeda suka tsoma baki cikin fadan ya kara tsananta halin da ake ciki a kasar.

Abin da ya faru ya nuna cewa, matakan soja da aka dauka, a maimakon ya daidaita rikicin da ake fuskanta, sai ma ya kara tsananta shi. Ban da haka, zaman rayuwar al'ummar kasar ma sai kara tabarbarewa yake yi. Kididdigar da MDD ta samar ta nuna cewa, fadan da ke addabar kasar Syria ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu 100. Wani rahoton da MDD ta gabatar a ranar 11 ga wata ya yi nuni da cewa, sakamakon rikicin da ya barke a watan Maris na shekarar 2011, mutane miliyan uku a kasar sun rasa ayyukan yi, a yayin da wasu miliyan bakwai suka rasa matsuguninsu. Ban da haka, kashi 29 cikin 100 na mazauna kasar ba su da ruwan sha mai tsabta. Rahoton ya kuma nuna cewa, sabo da rashin abubuwa masu gina jiki da kuma kulawa yadda ya kamata, yawan mutuwar jarirai a kasar ya karu daga kashi 14 cikin dubu a shekarar 2011 zuwa kashi 18 cikin dubu, ke nan akwai jarirai kimanin 9000 dake mutuwa a kasar a kowace shekara. Har wa yau, cututtukan da suka hada da cutar shan inna sun fara kunno kai a kasar. Halin da ake ciki ya nuna cewa, tashin hankalin da aka dade ana fuskanta a kasar ya raunata kasar kwarai da gaske, wanda har ya sa tattalin arzikin kasar da da bai bunkasa sosai ba ya kara komawa baya.

Amma abin farin ciki shi ne, a shekarar 2013, bisa kokarin da MDD da wasu kasashe suka yi, an kwantar da matsalar makamai masu guba da ta kusan kawo yaki tsakanin Amurka da Syria, abin da ya kyautata zaton jama'a a kan makomar kasar. Duk da haka, akwai sauran rina a kaba wajen daidaita matsaloli kwata kwata da kasar ke fuskanta.

Bisa ga shirin da kungiyar haramta makamai masu guba ta zartas a baya,cewa, ya kamata Syria ta lalata gaba dayan makamanta masu guba kafin ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2014, amma hakika wannan ba abu ne mai sauki ba a mawuyacin halin da ake ciki. Ban da haka, ko da yake an tabbatar da shirya taron kasa da kasa kan matsalar Syria a ranar 22 ga watan Janairu mai zuwa a birnin Geneva, amma har yanzu kasashen duniya da kuma bangarori daban daban na kasar Syria suna fama da sabanin ra'ayi a kan mutanen da suka cancanci halartar taron da kuma abubuwan da za a tattauna a wajen taron, har ma akwai 'yan adawa da har yanzu suka bayyana kauracewa taron, abin da ya janyo damuwar al'umma dangane da taron. Ban da haka, shekarar 2014 shekara ce da ake shirin gudanar da babban zabe a kasar ta Syria, kuma kafin wannan, shugaba Bashar al-Assad ya bayyana shirinsa na tsayawa takara, wanda a ganin manazarta yana da damar ci gaba da mulki a kasar, sai dai ko kadan 'yan adawa ba za su yarda da hakan ba. Don haka, ana iya cewa, idan har Bashar al-Assad ba zai yi watsi da shirinsa na tsayawa takarar ba, 'yan adawa za su yi iyakacin kokarin kauracewa zaben. Bugu da kari, da alamun cewa, a sabuwar shekara ta 2014, za a kara fuskantar matsala a kasar ta Syria.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China