Kamar yadda majiyar tsaro ta tabbatar wadansu matasa ne su biyu dauke da ababen fashewar suka dana shi bayan da suka nade jikin su a cikin kasuwan, wanda nan take ya hallaka mutane 10 yayin da wasu suka hallaka.
Bayan kai wadanda suka jikkata asibiti wasu daga cikin su daga baya sun mutu adadin da ya sa matattun ya kai 19, ciki har da matasan da suka kai harin su biyu.
Babu wani kungiyar ko mutumin da ya dauki nauyin harin, amma ma'aikatan leken asiri na kasar Kamaru sun tabbatar da cewar suna nuna yatsa ga kungiyar Boko Haram, kungiyar ta'addanci a Nigeriya da suke ta kai hari a jihar dake yankin arewa mai nisa. (Fatimah)