in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kasance kasa mai wadata da demokuradiyya da jituwa na tsari irin na gurguzu
2016-03-11 11:25:40 cri
Daya daga cikin wakilan jaridar Tribune ta kasar Kamaru da ke halartar taron kafofin watsa labarai na Sin da Afirka a kasar Sin, Godlove Bainkong ya gabatar da wani jawabi mai taken "Sin za ta kara samar da aikin yi ga mutane fiye da miliyan 10 a birane a shekarar 2016", inda ya mayar da hankali kan rahoton aikin gwamnati da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar a gun taro na 4 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12.

Bayanin ya dora muhimmanci ga batun samar da aikin yi a birane, yin rajistar yawan mutanen da ba su da ayyukan yi, bunkasuwar yawan GDP da yawan kudin shigi da fici, gina sabbin hanyoyin motoci a kauyuka, cimma burin kawar da matalauta fiye da miliyan 10, da tabbatar da ba da inshorar lafiya a dukkan kasar da dai sauransu.

Yana ganin cewa, idan har kasar Sin ta aiwatar da matakan da ta gabatar, tabbas ne za ta kasance kasa mai wadata da bin tsarin demokuradiyya da jituwa na tsari irin na gurguzu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China