in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan cinikayyar Sin ta Intanet zai zarta na sauran kasashe, in ji ministan kasuwanci
2015-12-28 10:18:31 cri

Alamu na cewa, yawan harkokin cinikayya ta Intanet na kasar Sin zai kai yuan tiriliyan 4, kwatankwacin dala biliyan 618 a wannan shekara, lamarin da zai zarce na sauran kasashen duniya

Ministan cinikayya na kasar Gao Hucheng ne ya bayyana hakan. Yana mai cewa, ya zuwa karshen wannan shekara, kasar Sin ta cimma manyan manufofin da ta tsara a cikin shirinta na raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 12, na zama kasar da ke kan gaba a harkar cinikayya.

Minista Gao ya ce, yanzu haka akwai sama da kasuwanni 80,000 da kasar Sin ke sayar da hajojinta baya ga kayayyakin yau da kullum na yuan tiriliyan 30 da take fatan sayarwa a wannan shekara, adadin da ake sa ran zai ba da gudummawar kimanin kashi 60 cikin 100 na yawan GDPn kasar.

Alkalluma na nuna cewa, a cikin shekaru biyar din da suka gabata, kayayyakin da kasar take fitarwa ya karu da 6.5 cikin 100 a ko wace shekara, yayin da jarin da ta zuba a kasuwannin duniya ya karu daga kashi 10.4 cikin 100 a shekara 2010 zuwa kashi 13.2 cikin 100 a shekara 2015.

Har ila yau, aikin hidima a bangaren harkokin cinikayya shi ma ya karu zuwa sama da kashi 13.6 cikin 100 a wannan shekara, lamarin da ba ta damar zama kasar da ke kan gaba wajen samar da hidima a duniya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China