Afrika ta Kudu: Kotun Pretoria ta zargi gwamnatin kasar da take doka ta hanyar hana cafke al-Bechir
Babbar kotun Pretoria ta bayyana cewa gwamnatin Afrika ta Kudu ta take doka ta hanyar yin watsi da umurnin kotun na hana shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir fita daga kasar a yayin taron kungiyar tarayyar Afrika (AU) da ya gudana a birnin Johannesburg. Dukkan shaidu sun nuna cewa gwamnatin Afrika ta Kudu ba ta girmama umurnin ranar 14 ga watan Yuni na babbar kotun Pretoria ba, wanda a cikinsa ya kamata gwamnatin kasar ta tsare mista al-Bashir a cikin kasar, in ji babban alkali, Dunstan Mlambo. (Maman Ada)