in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin shugaba Zuma
2015-12-17 09:40:29 cri

Dubban jama'a ne suka fito kwansu da kwarkwatansu suna zanga-zanga a manyan biranen kasar Afirka ta Kudu, inda suke zargin shugaba Jacob Zuma na kasar da almubazzaranci da dukiyar al'umma da kuma cin hanci.

Masu zanga-zangar dai sun bazama kan manyan tituna ne suna rera wakokin neman ganin an sauke shugaba Zuma daga mukaminsa tare da yin Allah-wadai da jam'iyyar ANC mai mulkin kasar.

A jawabin da ya yiwa dandazon jama'a a birnin Johannesburg, tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasar Zwelinzima Vavi, ya ce, sun fito a wannan rana ce, wato ranar hada kan kasa domin su fadawa kansu da kasar Afirka ta Kudu da ma duniya baki daya cewa, ba za su lamunci cin hanci ba.

Vavi ya zargi shugaba Zuma da yunkurin wargaza tattalin arzikin kasar, lamarin da ya haifar da mummunan rashin aiki da gurgunta tsarin tattalin arzikin kasar, kan matakin da ya dauka na canja ministocin kudi na kasar har sau biyu cikin mako guda kacal.

Shi ma shugaban jam'iyyar CPP Mosiuoa Lekota, ya zargi shugaba Zuman da tsunduma cikin harkar cin hanci, yana mai ba da misali da badakalar dala miliyan 23 da ake zargin shugaban ya yi amfani da su wajen kawata gidansa, baya ga cin hancin da ya yi katutu a kamfanoni mallakar gwamnati.

Rahotanni na cewa, an gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Zuma ce a biranen Johanesburg, da Pretoria, da Cape town, da Port Elizabeth da sauransu. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China