in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu: Mutane 250 suka jikkata a yayin da jiragen kasa suka ci karo da juna a Johannesburg
2015-07-18 13:13:13 cri
Kimanin fasinjoji 250 ne suka jikkata a ranar Jumma'a da yamma a yayin wani taho mu gama na jiragen kasa da ya faru a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu, in ji hukumomin wurin.

Hadarin ya faru a kusa da tashar Booysens da ke birnin. Ma'aikatar bada aikin jin kai ta bayyana cewa adadin wadanda suka jikkata na iya karuwa dalilin cewa har yanzu akwai wasu mutanen da suka makale a cikin taragogin jiragen kasan. Wasu daga cikin wadanda suka jikkata na cikin wani mawuyacin hali. A cewar wasu da lamarin ya faru a gaban idonsu, jirgin kasa ya ci karo da wani jirgin kasa kafin daga bisani ya jirkice kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China