in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afrika ta Kudu ya lashi takobin yaki da wariyar launin fata
2016-01-10 13:21:23 cri
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya yi alkawarin yaki da wariyar launin fata dake kokarin raba kasarsa a ranar Asabar.

Wadanda suka rungumi wariyar launin fata da wadanda suka kasance masu wariyar launin fata suna rayuwa ne a lokacin baya, in ji shugaba Zuma a gaban miliyoyin jama'a da suka taru a filin wasa na Royal Bafokeng Stadium na Rustenburg, da ke gundumar arewa maso gabashi, albarkacin cikon shekaru 104 na jam'iyyar ANC.

Ko shakka babu akwai wasu 'yan tsirarru a kasarmu da ke fatan raba al'ummomi da kuma suke biyayya ga tsoffin shugabannin lokacin wariyar launin fata, in ji Jacob Zuma. Inda ya kara da cewa, wadannan mutane basu wakilatar halayyar sabuwar kasar Afrika ta Kudu.

Afrika ta Kudu ta fara fuskantar wata guguwar wariyar launin fata bisa wasu kalaman wariyar launin fata da aka rika yayatawa a kan bakaken fata.

A makon da ya gabata, jam'iyyar ANC ta kai karar wasu 'yan Afrika ta Kudu gaban kotu da suka rika ambato kalaman wariyar launin fata bisa kafofin sadarwa, da suka hada da masanin tattalin arziki Chris Hart, da tsahon ma'aikacin dillancin gidaje Penny Sparrow da kuma kocin wasan lankwasa jiki Justin van Vuuren.

Al'amarin ya faru ne a lokacin da Penny Sparrow bisa kafofin sadarwa na kimanta bakaken fata da birrai da aka saki a jajibirin sabuwar shekara da ranar sabuwar shekara a wuraren shakatawa na jama'a.

Jam'iyyar ANC, a lokacin bikin cikon shekarunta 104, ta sake jaddada fatata na ganin wata al'umma mai cike da 'yanci da zaman lafiya inda babu wariyar launin fata.

Shugaba Jacob Zuma ya yi kira ga manyan kusoshin jam'iyyarsa da su rungumi halayya ta gari da kuma dukufa wajen yi wa kasa aiki, inda ya maida hankali kan adalci, aiki, kaunar jama'a da kuma yiwa talakawa aiki. Dole mu yi watsi da nuna son kai da cin hanci, ya kamata mu yi aiki tare domin kawar da cin hanci, in ji shugaba Zuma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China